Za ayi Salatul Gha’ib ga margayi Aminu Dantata a Kano

DA DUMI-DUMI: Za ayi Salatul Gha’ib ga margayi Aminu Dantata a Kano
Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta sanar da gudanar da Salatul Gha’ib ga marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Kannywoodstyle ta ruwaito Sanarwa daga Shugaban Majalisar, Malam Ibrahim Khalil , za’a gudanar da sallar ne da misalin karfe 2:00 na rana a masallacin Umar Bin Khaddab da ke Gyadi-Gyadi a Kano.
Ya tabbatar da shirye-shiryen da aka yi kuma ya yi kira ga al’umma Musulmi da su halarta domin yin addu’a ga mamacin.
Mamacin dai ya rasu ne a Dubai kuma za a yi masa sallah a Madina kamar yadda ya ambata a cikin wasiyyarsa….
Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
Alhaji Aminu Ɗantata shi ne mai kamfanin mai na Express Petroleum & Gas, kuma a matsayin uba yake ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote.