AlbumsLabaraiUncategorized
Alhaji Aminu Ɗantata Ya Rasu

Fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasu a daren ranar Juma’a, 27 ga Yuni, 2025, yana da shekaru 94 a duniya
Ɗantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata
Tsohon mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ce Kano da Najeriya sun yi babban rashin dattijo
Kano – Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata.
An sanar da rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar ne a safiyar ranar Asabar, kuma an ce ya rasu ne a daren ranar 27 ga Yuni, 2027
Kannywoodstyle ta fahimci cewa Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu ne yana da shekaru kusan 94, kuma ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa .